✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto karin Daliban Sakandaren Bethel 3 a daji

Kawo yanzu kimanin dalibai 80 na hannun masu garkuwar.

Karin dalibai uku daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a makarantar sakandaren Bethel Baptist sun kubuta daga hannun ’yan bindigar.

An ceto karin daliban ne a cikin daji, kwanaki kadan bayan wasu biyu sun kubuta daga hannun masu garkuwar.

Shugaban makarantar, Rabaran Adamu Jangado, ya tabbatar wa wakilinmu ta wayar tarho cewa jami’an tsaro sun gano daliban ne a Daji Kakuma da ke Jihar, suka kuma ceto su a ranar Talata.

Rabaran Adamun, wanda kuma shi ne mai makarantar bai yi wa wakilin namu karin bayani ba.

Kakakin ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, ya tabbatar da kubutar da karin daliban, amma ya ce hukumar makarantar ba ta sanar da su a hukumance ba.

A ranar 5 ga watan Yuli, 2021 ne ’yan bindiga suka kutsa makarantar sakandaren Bethel Baptist da ke kan hanyar Kaduna zuwa Kachi, suka sace dalibai 121.

A kwanakin bayan masu garkuwar sun sako 28 daga cikin yaran bayan iyayensu sun biya kudin fansa.

Kawo yanzu dai mutum 80 daga cikin yaran ne ke hannun masu garkuwar.