✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto mahaifiyar dan takarar Sanata a Kano daga hannun ’yan bindiga

Jami'an hukumar DSS sun kubutar da ita a Jigawa bayan ’yan bindigar sun ce tana Katsina

’Yan bindiga da suka yi garkuwa da mahaifiyar dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya, Abdulsalam Abdulkarim Zaura, wanda aka fi sani da AA Zaura.

AA Zaura ya tabbatar da sako mahaifiyar tasa, mai suna Hajiya Laure, tare da bayyana godiyarsa ga jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen ganin an sako ta.

“Ina godiya ga hukumar tsaro ta DSS da sojojin sama da ’yan sanda da sibil difens kan yadda suka tashi haikan wajen ganin sun kubutar da mahaifiyata.

“Wannan ba zai hana ni ci gaba da yin ayyukan alheri da nake yi a Kano ba; a matsyina na Musulmi, na yi imani cewa dole zan fuskanci jarabawa iri-iri,” inji dan takarar sanatan.

Shi ma da yake tabbatar da sako Hajiya Laure, Shugaban Karamar Hukumar Ungoggo ta Jihar Kano, Abdullahi Garba Ramat ya ce jami’an hukumar tsaro ta DSS ne suka kubutar da dattijuwar a Jihar Jigawa kuma tuni aka mayar da ita ga iyalanta.

“Alhamdullah, an kubutar da Hajiya Laure -mahaifiyar AA Zaura, wadda aka yi garkuwa da ita, cikin koshin lafiya!! Hakika addu’o’i na kawo sakamako mai ban al’ajabi.

“Tana raye kuma cikin koshin lafiya kuma tuni jami’an DSS suka dawo da ita Kano kuma babu wanda ya biya kudin fansa, jami’an tsaro ne suka kubutar da ita,” kamar yadda ya wallafa ta shafinsa na Facebook.

A ranar Litinin da sanyin safiya ne dai wasu ’yan bindiga uku a kan babura suka yi dirar mikiya a gidan mahaifiyar AA Zaura, mai suna Hajiya Laure, suka yi awon gaba da ita.

Bayan harin da suka kai wa Hajiya Laure a gidanta da ke garin Zaura a Karamar Hukumar Ungoggo ta Jihar Kano, baga baya ’yan bindiga sun kira iyalan dattijuwar cewa sun kai ta Jihar Katsina.