✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mata masu juna-biyu 10 daga masana’antar kyankyasar jarirai a Ribas

'Yan sanda na kuma neman wadanda suka taba sayen jarirai daga gidan

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ribas ta ce ta ceto wasu mata masu juna-biyu su 10 yayin wani samame da ta kai wasu gidajen kyankyasar jarirai biyu da ke Jihar.

Kakakin rundunar a Jihar, SP Grace Iringe-Koko, ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar a Fatakwal, babban birnin Jihar ranar Talata.

Ta kuma ce rundunar ta sami nasarar kama wasu mutum hudu da ake zargin suna da hannu a cikin aika-aikar,

Grace ta kuma ce mutanen da aka ceto sun hada da maza biyu da mata masu juna-biyu su 10, ciki har da ’yan mata, wadanda aka ajiye a gidajen da karfin tsiya bayan an yi musu romon baka.

A cewarta, “Da misalin karfe 4:45 na yammacin ranar bakwai ga watan Janairun 2023, mun sami bayanai daga wasu majiyoyi masu tushe kan ayyukan wasu masu safarar kananan yara a yankunan Igwuruta da Omagwa da ke Jihar.”

Kakakin ta kuma ce masu juna-biyun da aka ceto ’yan tsakanin shekara 15 zuwa 29 ne.

Ta kuma ce bincikensu na farko-farko ya nuna cewa idan matan sun haihu, mamallakin gidan kan dauke jariran sannan ya biya su Naira 500,000.

Ta ce tuni aka tura lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar, yayin da ake ci gaba da farautar wadanda suka riga suka sayi jarirai daga gidan. (NAN)