✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto mutum 100 da ’yan bindiga suka sace a Zamfara

Aikin ceton ya dauki lokaci ne saboda yawan wadanda aka sace.

Rundunar ’yan sanda a Jihar Zamfara ta sanar da ceto mutum 100 da ’yan bindiga suka sace a yankin Dansadau da ke cikin yankin Karamar Hukumar Maru.

’Yan sandan sun ce mutanen sun shafe fiye da kwana 40 a hannun ’yan bindagar kafin ceto su a ranar Litinin ta hanyar sa bakin tubabbu da gwamnatin jihar ta yi sulhu da su.

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Mohammed Shehu ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa, ’yan bindigar sun sace mutanen ne a kauyen Manawa tun a ranar 8 ga watan Yunin da ya gabata.

Bayanai sun ce mutanen da aka yi garkuwa da su a wani daji na Kabaru sun shafe fiye da kwana 40.

“Wannan ceto na daya daga cikin kokarin rundunar ’yan sandan jihar na ganin an kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

“Tun lokacin da abin ya faru rundunar ta tashi tsaye da hadin gwiwar ma’aikatar tsaro da sauran masu ruwa da tsaki na al’umma da suke taimaka mana wajen samar da zaman lafiya.

“Aikin ceton ya dauki lokaci ne saboda yawan wadanda aka sace din, dole sai an tsara an yi amfani da ilimi da dabara don gudun samun matsala wajen kubuto da su din, kuma Alhamdulillah komai ya tafi daidai.

SP Shehu ya kara da cewa duk da dai mutum 100 aka sace a yanzu 80 ne da aka ceto ke hannun jami’an tsaro.

“Sauran 20 ba za su iya zuwa ba saboda yanayi na rashin lafiya ya sa ba za su iya zuwa Gusau ba sai muka mika su ga iyalansu don su kula da su wajen samo musu lafiya.