✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 122 da N81.3m daga gobara a Kano

Mutum 20 sun rasa rayukansu a gobara daban-daban da ta faru a watan Maris.

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta ceto mutum 122 da kudi N81.3 daga gobara 116 da aka samu a watan Maris a Jihar.

Kakakin hukumar, Saminu Abdullahi ne ya bayar da alkaluman cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Juma’a.

“Mun samu damar kai dauki ga kiran waya 88 da kuma na bogi 22 daga mutane daban-daban,” inji shi.

Ya ce mutum 20 sun rasa rayukansu, sai kuma kudi kimanin miliyan 36.9 da suka salwanta a sanadiyar gobara a jihar.

Abdullahi, ya ce da yawancin gobarar da aka samu a jihar na faruwa ne sakamakon rashin iya sarrafa gas din girki da kayan laturoni.

Har wa yau, ya ja hankalin mutanen jihar da su zama masu kula da dukkannin abin da ya shafi kayan wuta.