✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 30 a hatsarin jirgin Kebbi

Masu aikin ceto sun gano gawa 46 bayan hatsarin jirgin ruwa a Jihar Kebbi.

An ceto kimanin mutum 30 da ransu daga cikin fasinjoji kusan 200 da jirgin ruwa ya kife da su a Jihar Kebbi.

Suleman Bobo daga cikin masu aikin ceto ya ce an kuma gano gawarwaki 46 da suka nutse bayan hatsarin jirgin da ke dauke da mutanen da yawancinsu masu sana’ar hannu ne da ’yan kasuwa.

“Kawo yanzu an gano gawarwaki 46, an kuma binne su, banda wadanda aka ceto a cikin dare,” inji Suleiman wanda shi ne Shugaban matasa garin Warra.

Suleman ya ce 23 daga cikin gawarwakin an gano su ne a garin, sauran kuma a wasu kauyukan da ke makwabtaka da su.

Ya shaida mana cewa a ranar Laraba, an gano gawarwaki biyar, a ranar Alhamis kuma an gano wasu 41.

Aminiya ta gano cewa masu aikin ceto ne suka gano 45 daga cikin gawarwaki, ta karshe kuma an gano ta ne bayan da ruwa ya dago ta.

Wakilinmu ya ziyarci wurin da ake aikin ceton bayan aukuwar hatsarin, inda ya iske daruwawan matasan garin na Warra suna kai-komo wajen gudanar da aikin ceto.

Jirgin ruwan ya kife da fasinjojin ne a yankin Tsohuwan Lambata da ke Karamar Hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi a hanyarsa ta kai  fasinjojin Jihar Neja.