✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An ceto mutum 7 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna

An yi musayar wuta tsakanin ’yan bindigar da dakarun tsaro.

Dakarun Tsaro sun kubutar da wata uwa da ’ya’yanta uku da wasu karin mutum uku daga hannun ’yan bindiga a Jihar Kaduna.

Dakarun Tsaro na Operation Forest Sanity sun yi nasarar kubutar da mutanen bakwai yayin wani aikin sintiri a tsakanin yankunan Birnin Gwari zuwa Chikun.

Wannan dai na kunshe cikin wata sanarwa da Kwamshinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya wallafa a shafinsa na Twitter.

A cewarsa, Gwamnatin Kaduna wadda ta yaba wa kwazon dakarun, tuni ta damka mutanen hannun makusantansu.

Sameul Aruwan ya ce dakarun tsaron sun yi nasarar kubutar da mutanen ne lokacin da suke sintiri a kan titin Birnin Gwari zuwa Gayam zuwa Kuriga zuwa Manini.

Ya ce ’yan bindigar sun bude musu wuta, inda su kuma suka mayar da martani nan take tare da murkushe maharan, wadanda suka tsere cikin daji.