✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci gaba da sauraron shari’ar kisan Ummita

Kotun ta ci gaba da karbar shaidu a shari'ar bayan ta saurari bayanan mahaifiya da kuma kanwar marigayiya Ummita a ranar Laraba.

A ranar Alhamis kotu ta ci gaba da sauraron shari’ar kisan matashiyar nan, Ummukulsum Sani Buhari, waddda ake zargin masoyinta dan kasar China, Geng Quangrong ya kashe a Kano.

Kotun ta ci gaba da karbar shaidu a shari’ar bayan ta saurari bayanan mahaifiya da kuma kanwar marigayiyar a ranar Laraba.

Da suke bayar da shaida a ranar Laraba, kanwar marigayiyar da mahaifiyar sun siffanta wa kotun yadda wanda ake zargin ya yi mata kisan gilla a cikin dakinta, a kan idansu.

A ranar Alhamis ake gabatar da karin shaidu daga makwabta da sauran mutanen suka halarci wurin da abin ya faru, domin kafa hujja a kan tuhumar da ake wa dan Chinan.

Rahotanni sun nuna Mista Geng ya shekara kimanin biyu suna soyayya da Ummita, da nufin zai aure ta, kafin daga bisani ya yi mata kisan gilla a gidan iyayenta da ke unguwar Jan-Bulo a Kano.

Wata sabuwar dambarwa ta da kunno kai a shari’ar a ranar Laraba, ita ce ikirarin wanda ake tuhuma cewa ya tura wa marigayiyar Naira miliyan 117 ta banki domin sayayyar shirye-shiryen aurensu.

Lauyansa, ya kuma kara da cewa ya yi mata sayayyan sarkoki na sama da Naira miliyan uku, baya ga kudin kashewa Naira dubu dari da yake ba ta a kowane mako.

Sai dai ko da lauyan nasa ya yi  wa kanwarta Asiya tambaya game da wadannan kudade, ta bayyana wa kotun cewa ita ba ta da masaniya a kansu.