✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ci gaba da shari’ar nadin Sarkin Zazzau

Kotu ta umarci kowane bangare ya tsaya a matsayinsa na yanzu zuwa lokacin da za ta yanke hukunci

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya, ta ci gaba da sauraron shari’ar da Iyan Zazzau Alhaji Bashir Aminu ya shigar, yana kalubalantar nadin da aka yi wa Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

A zaman kotun na ranar Talata, 27 ga Oktoba, 2020, alkalin kotun, Mai shari’a Kabir Dabo ya umarci bangarorin da ke shari’ar da kowannensu ya tsaya a matsayinsa na yanzu har sai ta yanke hukunci.

“Lauyoyin gwamnati na da wasu koke amma ba su gabatar wa kotu ko masu shigar da kara ba, don haka suka nemi a daga kuma mun yarda a yi hakan.

“Kotu ta ce kar kowa ya taba wannan kujera ko abin da zai taba kujerar har sai ta ba da umarninta”, inji lauyan masu kara, Yunus Ustaz Usman SAN, bayan zaman kotun.

Bayan ya saurari lauyoyin masu shigar da kara karkashin jagorancin Yunus Ustaz da na wadanda ake kara da Sunusi Usman ke jagoranta, kotun ta dage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga watan Nuwamba.

Lauyan masu karar, ya ce suna kalubalantar hanyar da aka bi ne tunda ba a bi al’adar Masarautar Zazzau ba kuma wanda aka nada ba ya cikin wadanda masu zaben Sarki suka zaba.

Idan ba a manta ba masu karar sun garzaya kotu ne suna kalubalantar nadin da Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi wa Bamalli, inda suka nemi kotun ta soke nadin.

Suna rokon kotun ta ayyana Alhaji Bashir Aminu a matsayin halastaccen Sarkin Zazzau wanda ya fi samun yawan kuri’u a zaben da Masu Zabar Sarki a Masarautar suka yi bisa tsarin da aka sani tun shekaru aru-aru.