✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage ranar fara daukar ma’aikata 774,000

An dage daukar ma’aikata 1,000 a kowac karamar hukuma zuwa ranar 1 ga watan Nuwamba

Gwamnatin Tarayya ta dage ranar da za ta fara daukar ma’aikata 1,000 a kowacce daga hukumomin Najeriya 774 zuwa 1 ga watan Nuwamba.

Minista a Ma’aikatar Kwadago da Samar da Ayyuka, Festus Keyamo a cikin wata sanarwa ya ce Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne ya amince da dagewar.

Shirin na yunkurin samar wa matasa 774,000 ayyukan taimakon yankunansu na tsawon watanni uku.

Ministan ya ce amincewa da bukatar ta biyo bayan wasikar da aka aike wa shugaban ta sanar da shi cewa har yanzu akasarin wuraren da za a yi ayyukan na cike da ruwa saboda damuna.

Keyamo ya ce an tsara aiwatar da shirin a cikin rani ne saboda sannan ne ake sa ran dukkannin wuraren za su kasance babu wani kalubale a tare da su.

Sai dai ya ce an ci gaba da daukar bayanan ma’aikatan da za a dauka aikin ta hanyar wasu bankuna ba tare da wani tsaiko ba a duk fadin kasa.

Sanarwar ta kuma ce, “Domin samun karin bayani kan bankunan da aka ware wa kowace karamar hukuma domin shirin, sai a ziyarci shafin shirin a www.specificpublicworks.gov.ng.”

Ministan ya kara da cewa akwai sauran karin bayani a shafin kan kwamitin da aka nada a kowacce jiha domin tantancewa da zabar wadanda za su shiga cikin shirin na daukar ma’aikata.