✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dage ranar fara rajistar jarabawar JAMB ta 2022

Hukumar dai ta dage wa'adin ne da mako daya, don yin wasu gyare-gyare.

Hukumar da ke Kula da Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) ta dage ranar fara rajistar jarrabawar shekarar karatu ta 2022 /2023.

A baya dai hukumar ta tsayar da ranakun 12 zuwa 19 ga watan Fabrairun 2022 domin fara rajistar, amma yanzu ta dage ta zuwa tsakanin 19 da 26 ga watan na Fabrairu.

Shugaban sashen kula da hulda da jama’a na kamfanin, Dokta Fabian Benjamin, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a madadin hukumar ranar Talata.

Ya ce karin na mako daya an yi shi ne domin a samu damar inganta hanyoyin yin rajistar ta yadda mutane za su samu damar yi cikin sauki.

Dokta Fabian ya ce suna sa ran za a kammala aikin a cikin mako dayan, kuma za  a yi amfani da lokacin wajen karbar korafe-korafe daga dalibai masu rajistar da ma sauran masu ruwa da tsaki a harkar jarabawar.

Hukumar dai ta ce za ta wallafa sabbin sauye-sauyen da aka samu shi a shafinta ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairun 2022, a cikin rahoton da take wallafawa a kowanne mako.

JAMB ta kuma shawarci daliban da su ci gaba da bibiyar tsarin rajistar na hukumar domin sanin sabbin tsare-tsaren da take fitowa da su.