✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dage shari’ar dan Chanar da ake tuhuma da kashe Ummita

An dage zaman kotun zuwa 27 ga watan Oktoba.

An dage shari’ar dan Chanar da ake tuhuma da kashe matashiyar nan Ummukulsum Sani Buhari wadda aka fi sani da Ummita a Jihar Kano.

An dage zaman kotun har sai an samarwa da Mista Geng Quangrong, wanda zai yi masa tafinta daga turanci zuwa Chanisanci.

Ba a jima da fara zaman kotun ba ne aka dage zaman saboda matsalar rashin fahimtar bayanai daga bangaren Mista Geng, wanda ake zargi da kisan Ummita a Kano.

A Talatar nan ce dai aka ci gaba da sauraran shari’ar a gaban Babbar Kotun Jihar Kano karkashin jagorancin Mai sharia Sunusi Ado Ma’aji .

A zaman kotun, lauyan wanda ake tuhuma Barista Balarabe Muhammad Dan Azumi ya roki kotun ta samar da wanda zai rika fassara wa wanda ake tuhuma bayanan kotu cikin harshensa na Chanisanci.

“Kamar yadda tsarin mulkin kasa ya ba da dama cewa duk wani mutum da ake tuhuma yana da damarmaki kamar yadda sashe na 36 da ya tanadi cewa dole ne a kawo shi kotu sannan a tambaye shi da harshen da ya fi fahimta.

“Sannan yana da dama a kawo masa wanda zai riqa gaya masa abin da ake nufi.

“Ita kuma dokar tsarin mulkin kasa a gaba take da kowacce doka.”

Lauyan Gwamnati kuma Kwamishinan Shari’a Barista Musa Abdullahi Lawan bai yi suka game da wannan roko ba.

A cewar Barista Lawan, dama tuni suka yi rubutu na neman wanda zai rika yi masa fassara kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasa ya bada dama.

A karshe dai Mai Ma’aji ya bayar da umarnin samo wanda zai yi wannan aiki na tafinta cikin harshen Chanisanci tare da dage zaman kotun zuwa 27 ga watan Oktoba 2022.