✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da ‘abokan cin mushen’ Abba Kyari daga aiki

An dakatar da yaran Abba Kyari daga aiki, ana neman wanda ya tsere ruwa a jallo

Hukumar Aikin Dan Sanda ta Najeriya ta dakatar da yaran DCP Abba Kyari da aka kama su tare a kan badakalar hodar Iblis nan take.

Hafsoshin biyu da aka dakatar su ne ACP Sunday Ubua, da kuma ASP James Bawa, wadanda da ma can suna aiki ne kai-tsaya a karkashin Abba Kyari rundunar IRT da yake jagoranta.

Sanarwar Hukumar ta kara da cewa, “Ana umartar Sufeto-Janar na ’Yan Sanda ya sani cewa Abba Kyari da dama can an dakatar da shi zai ci gaba da kasancewa a hakan tare da sauran biyun, har sai an kammala duk binciken da ake yi.”

Ta kara da dakatar da Insfekta Simon Agrigba da Infketa John Nuhu daga aiki, sannan ta sa a kamo Insfekta John Umoro da ya tsare, a kuma sanar da hukumar.

Ana zargin ACP Ubua da ASP Bawa suna da hannu kai tsaye a badakalar hodar Iblis da aka tsare Abba Kyari a kai a baya-bayan nan.

Hukumar ta sanar da dakatar da su ne da wata sanarwa da ta aike wa Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya a ranar 16 ga watan Fabrairu, dauke da sa hannun Mai Sharia’a Clara B. Ogunbiyi a madadin Shugaban Hukumar, Musiliu Smith.