✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Buhari ya dakatar da darektocin EFCC

An dakatar da darektoci 12 da wasu manyan jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC daga aiki nan take. Ofishin Atoni Janar…

An dakatar da darektoci 12 da wasu manyan jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC daga aiki nan take.

Ofishin Atoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya sanar da dakatarwar a cikin sakon da ya aike wa mukaddashin shugaban hukumar EFCC, Mohammed Umar a daren Talata.

Dakatar da manyan jam’ian na EFCC ya biyo bayan binciken da kwamitin da shugaban kasa ya kafa ke yi ka zargin dakataccen mukaddashin shugaban hukumar Ibrahim Magu.

Wata majiya ta ce kwamitin na tsohon Mai Shari’a Ayo Salami “ya bukaci a dakatar da dukkan darektocin EFCC domin ya binciki ayuukan hukumar. An sanar da dakatar da darektocin da manyan jami’an hukumar nan take ne a narar Talata”.

Cikin wadanda dakatarwar ta shafa har da sakataren hukumar Olanipekun Olukoyede.

Tun a makon jiya kwamitin binciken ke ta yi wa Magu wanda ke tsare a hannun jami’an tsaro tambayoyi, kan zargin karkatar da wasu kadarorin gwamnati da aka kwato.

Zargi 22 da Magu yake fuskanta sakamakon korafin da ministan shari’a ya rubuta wa shugaban kasa sun sa aka dakatar da shi tare da gayyatar darektoci da manya-manyan jami’an hukumar su gurfana a gaban kwamitin domin yin bayanai.

Kakakin Ministan Shari’a, Umar Jibrilu Gwanadu ya sanar da dakatar da Magu domin ba kwamitin damar gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen.

Daga bisani mai magana da yawun Shugaban Kasa Garba Shehu ya ce hakan shi ne ya fi dacewa domin tabbatar da gaskiyar lamarin.