Daily Trust Aminiya - An dakatar da Kwamandan Hisbah kan karkatar da kayan tallafi
Subscribe

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah na Jihar Kano, Sheik Harun Ibn Sina

An dakatar da Kwamandan Hisbah kan karkatar da kayan tallafi

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta dakatar da kwamandanta na karamar hukumar Dala, Suyudi Hassan Muhammad.

Kwamandan Hisbah na jihar, Ustaz Ibn Sina ne ya dakatar da Suyudi bisa zargin karkatar da kayan tallafin COVID-19.

Sanarwar da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, Ibrahim Lawal Fagge ya fitar ce an dakatar da Suyudi Hassan ne na tsawon wata daya.

Hakan na zuwa ne bayan ranar Juma’a an tashi baram-baram a zaman neman maslaha da aka yi da wadanda suka yi korafin da wanda ake zargin da karkatar da kayan tallafin da aka ba su su raba wa jama’a.

More Stories