✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da malaman makarantun da suka yi yajin aiki a Zimbabwe

Malamai sun shiga yajin aikin neman karin albashi a ranar da aka bude makarantu

Ma’aikatar Ilimi ta kasar Zimbabwe ta dakatar ta malaman makarantun da suka yi yajin aiki a ranar da dalibai suka koma makarantu.

Malamai da yawa a makarantun gwamnati a kasar sun yi yajin aiki ranar Litinin saboda karancin albashi.

An dakatar da malaman ne bayan sun shafe wata uku ba tare da an biya su albashi ba.

Gwamnatin Zimbabwe ta ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin rashin da’a da malaman da aka dakatar suka nuna.

Sai dai dakatar malaman bai yi mutane da dama dadi ba, inda wasu ke ganin hukuncin a matsayin rashin adalci.

Kungiyar malaman ta shiga yajin aikin ne tana neman a rika biyan su mafi karancin albashi na Dala 540.

Yawancin malaman makaranta a kasan ana biyan su kasa da Dala 200 a farashin gwamnati, wanda bai kai Dala 100 a kasuwar bayan-fage be, wadda yawanci da farashinta ake sayar da kaya da biyan ayyuka a kasar.

A ranar Talata gwamnati ta sanar da karin albashin ma’aikatanta da kashi 20 cikin 100, wanda ya hada da biyan su Dala 100 a wata.

An koma makarantu a kasar Zimbabwe ne a ranar Litinin bayan hutun wata daya a sakamakon cutar COVID-19.