✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da matuka jirgi saboda bai wa hammata iska a sararin samaniya

Fadan nasu dai bai shafi sufurin jirgin ba.

An dakatar da aikin wasu matuka jirgin saman kamfanin Air-France biyu sakamakon bai wa hammata iska da suka yi cikin jirgi.

Matukin jirgin da mataimakinsa sun ba gwada kwanji yayin da suke tuka jirgi kirar Airbus A320 daga Geneva zuwa Paris a watan Yuni kamar yadda jaridar Swiss News Outlet ta shaida.

Ma’aikatan jirgin sun shiga tsakani inda daya daga cikin ma’aikatan ya tsaya tare da matuka jirgin har sai da jirgin ya sauka ba tare da matsala ba.

BBC ya ruwaito cewa fadan nasu dai bai shafi sufurin jirgin ba kamar yadda kamfanin jirgin ya tabbatar.

Lamarin kuma ya faru ne bayan wallafa wani rahoto da hukumar da ke bincike kan sufurin jiragen sama ta Faransa ta yi da ya ce kamfanin jirgin yana sako-sako game da tsare-tsarensa na tsaro.