✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da Nuru Khalid daga limancin Juma’a saboda caccakar Buhari

Kwamitin ya ce hudubar malamin ta saba da addinin Musulunci

Kwana daya bayan yi wata zazzafar hudubar da ya caccaki gwamnatin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari kan matsalar tsaro, Kwamitin Masallacin Apo da ke Abuja, ya dakatar da Sheikh Nuru Khalid daga limancinsa.

Rahotanni sun ce Sheikh Nuru Khalid a cikin hudubarsa ta ranar Juma’ar da ta gabata, ya caccaki gwamnati kan gaza magance matsalar tsaro da kuma yawaitar kashe-kashe a Najeriya.

Sashen Hausa na BBC ya rawaito cewar a cikin hudubar, malamin ya fadi matakin da ya kamata talakawa su dauka idan har gwamnati ta bari aka ci gaba da kashe su, ta hanyar kin fitowa zabe.

“Sharadin talakan Najeriya ya zama guda daya kawai, ku hana kashe mu, mu fito zabe, ku bari a kashe mu, ba za mu fito zabe ba, tun da ku ba abin da kuka sani sai zabe,” inji Sheikh Nuru Khalid a hudubar tasa.

Sai dai a cikin wani sako da shugaban kwamitin Masallacin, Sanata Sa’idu Muhammed Dansadau ya aika wa BBC, ya ce sun dakatar da Malamin daga yin limanci saboda hudubar malamin da kwamitin ya kira ta tunzura jama’a.

Sanarwar ta ce, “Ina mai sanar da kai cewa an dakatar da kai daga Limamanci a Masallacin ’yan Majalisar da ke shiyyar Apo Abuja daga yau 2/4/22 har zuwa wani lokaci.

“An dauki wannan matakin ne saboda hudubar Juma’ ta tunzurawa a ranar 1/4/22 inda ka ba mutane shawarar kada su yi zaɓe a 2023 har sai ’yan siyasa sun amsa wasu tambayoyi.

“Ya kamata a ce ka ba su shawara su fito zaɓe don kawar da wadanda suka saba wa Allah, da masu zabe da kuma kasa,”

Kwamitin ya ce hudubar Sheikh Nuru Khalid ta saba wa addinin Islama.

Kazalika, a cikin sanarwar, kwamitin ya nada sabbin lamamai na Masallacin inda Malam Mohammad zai yi tafsiri, yayin da kuma Malam Abdullahi zai jagoranci Juma’a.

Babu wani martani daga Sheikh Nuru Khalid game da matakin da kwamitin ya ɗauka na dakatar da shi, kuma BBC ta yi ƙoƙarin tuntuɓar malamin amma wayarsa a kashe.

Sheikh Nuru Khalid ya sha caccakar gwamnati kan tabarbarewar tsaro a Najeriya, kuma hudubarsa na zuwa ne bayan harin da ’yan bindiga suka kai wa jirgin kasa a ranar Litinin inda har yanzu ba a san adadin mutanen da suka kashe ba da waɗanda suka sace.