✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dakatar da Sakataren Hukumar alhazan Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da dakatar da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Alhaji Abubakar Babangida Tafida. Wata sanarwa mai…

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya amince da dakatar da Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar, Alhaji Abubakar Babangida Tafida.

Wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mai ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai, Mukhtar Gidado, ta ce dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

Sanarwar ta ce an riga an sanar da Babban Sakataren Hukumar a cikin wasikar da Sakataren Gwamnatin Jihar ya sanya wa hannu ranar 14 ga Satumba.

Ta kara da cewa an umarci Babban Sakataren da aka dakatar da ya mika lamuran hukumar ga babban jami’in hukumar mafi girma bayansa, har zuwa lokacin fitowar sakamakon binciken da gwamnatin jihar ta kaddamar a kan harkokin hukumar.