✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Fashin aiki: An dakatar da shugabannin makarantu 5 a Yobe

Fashinsu da na dalibai ya sa aka dakatar da su daga bakin aiki.

Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Yobe ta dakatar da shugabannin makarantu mallaki gwamnati jihar guda biyar daga aiki.

An dakatar da shugabannin makarantun ne bayan ziyarar ba-zata da Kwamishinan Ilimin Jihar Yobe, Dokta Muhammad Sani Idris, ya kai makarantun, amma bai same su a bakin aiki ba.

Manayan makarantan kwanan da kwamishinan ya ziyarta sun hada da GSS Damaturu da GSS Babbangida da GSS Gulani da GSS Bularafa.

A lokacin ziyarar ta ranar 6 ga Satumba, 2021, domin gwada kwazon malamai da duba yanayin koyarwarsu, kwamishinan bai iske dalibai sosai ba, su kansu shugabanin makarantun ba su zo aiki ba.

Sanarwar dakatarwar da ta fara aiki daga ranar 9 ga Satumba, ta umarci Mataimakan Shugabannin Makarantun da su ci gaba da jan akalan makarantun.

Dokta Sani Idris, ya bayyana takaicinsa kan abin da ya gani na rashin zuwan dalibai makaranta; Dalibai kadan din ma da ya sa samu a wadanda suke rubuta jarrabawar kammala sakandare (SSCE) ne.

Sannan a duk makarantu biyar din da ya ziyarta babu inda ya samu shugaban makaranta a ofishinsa.

Ya kuma da duba azuzuwa da dakunan kwanan dalibai da dakunan dafawa da cin abinci da sauran bangarori na makarantun.

Dokta Idriss, yace ma’aikatar ba za ta lamunci rashin zuwan shugabanin makarantu aiki ba saboda shi ke haifar da fashin dalibai, don haka gwamnati ba za ta zuba ido tana ganin hakan ya ci gaba ba.

Bayan nan ne ya umarci shugabanin makarantun da ba su halarci wajen aikin ba su gaggauta kai kan su zuwa ma’aikatar ilimi don bayyana dalilansu na kin zuwa aiki.

A cewarsa, daga yanzu zai ci gaba da kai irin wannan ziyara ta ba-zata a daukacin makarantun jihar dan ganin kwazo malamai da jajircewarsu a kan aiki da ma su kansu shugabanin makarantun.