✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakatar da ’yan Majalisar Zamfara kan alaka da ’yan bindiga

’Yan majalisar jihar sun yi rantsuwa da Al-Kur'ani don nesanta kansu da alaka da ’yan bindiga.

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta dakatar da mutum biyu daga cikin mambobinta bisa zargin su da alaka da ayyukan ’yan bindiga.

Sanarwar da majalisar ta fitar ta ce mambobin da aka dakatar su ne Hon. Yusuf Muhammad Anka mai wakiltar mazabar Anka da kuma Hon. Ibrahim T. Tukur Bakura mai wakiltar mazabar Bakura.

“Za su hallara a gaban kwamitin tsare-tsaren majalisa da kuma hukumomin tsaro da doka ta ba wa hakkin gudanar da bincike,’ inji sanarwar da majalisar ta fitar.

Sanarwar mai dauke da sa hannun Darakta Janar na Yada Labaran Majalisar, Mustapha Jafaru Kaura, ta ce an dakatar da ’yan majalisar da ake zargi da akala da ’yan bindiga ne na tsawon wata uku, kafin a kammala bincike kan zargin.

“Wadannan na daga cikin abubuwan da majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta cim ma matsaya a kansu a zamanta da Shugabanta, Rt. Hon. Nasiru Mu’azu Magarya, ya jagoranta,” inji shi.

Hakan ya biyo bayan an sa kowane dan majalisar ya yi rantsuwa da Al-Kura’ani domin nesanta kansa da alaka da ’yan bindiga a jihar.

A lokacin zaman majalisar, mamba mai wakiltar mazabar Maru ta Arewa, Honorabul Yusuf Alhassan Kanoma, ya shaida wa zauren majalisar cewa akwai zargi mai karfi a kan mambobin biyu, cewa suna da alaka da ayyukan ’yan bindiga, don haka jazaman ne majalisar ta dauki mataki.

A cewar Hon. Kanoma, a lokacin da aka sace mahaifin Shugaban Majalisar, an ga Hon. Yusuf Muhammad Anka da Hon. Ibrahim T Tukur Bakura suna murna da faruwar hakan.

Ya kuma zarge su da hada baki ta wayar tarho da ’yan bindigar da suka kashe tsohon dan majalisar jihar mai wakiltar mazabar Shinkafi, Hon. Muhammad G. Ahmad (Walin Jangeru).

Hon. Kanoma ya bukaci hukumomin tsaro su kwace wayoyin ’yan majalisar su bi diddigin duk wayoyin da suka yi, zauren majalisar kuma ya dakatar da su na tsawon wata kuku, kafin a kammala bincike a kansu.

Shi ma da yake tsokaci, dan majalisa mai wakiltar mazabar Birnin Magaji, Nura Dahiru Sabon Binin Dan Ali, ya goyi bayan shawarar ta Hon. Kanoma, da cewa bai kamata a bari duk kokarin da aka yi na tattaunawa da shugaban ’yan bindiga Bello Turji domin kubutar da mahaifin shugaban majalisar ya kare a banza ba — dole a hukunta masu hana zaman lafiya a jihar.

Bayan sauraron jawabansu, Shugaban Majalisar, Nasiru Mu’azu  Magarya, ya amince a dakatar da wadanda ake zargin, sannan ya sauke su daga shugabancin kwamitocin da suke jagoranta.

Daga nan sai ya nada Hon. Kanoma ya zama mai kula da Kwamitin Ayyuka da Sufuri wanda Hon. Anka yake jagoranta, shi kuma Hon. Nasiru Atiku Gora zai kula da Kwamitin Jinkai, wanda Hon. Bakura ke jagoranta.

Shugaban Majalisar ya kuma ba wa kwamitin tsare-tsare, wanda Hon. Kabiru Hashimu Dansadau yake jagoranta, wa’adin wata uku ya kammala bincike sannan ya gabatar da rahotonsa.

Wakilinmu ya yi kokarin ji daga bangaren ’yan majalisar da aka dakatar kan zargin su da alaka da ’yan bindiga, amma hakan bin yiwu ba, har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoto.