✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja harin ‘bom’

Sanata Shehu Sani ya ce jirgin ya kusa sauka daga kan hanyarsa, amma Allah Ya kiyaye.

Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ya taka bom din nakiya da ’yan bindiga suka dasa a titinsa, sa’o’i kadan bayan sun bude wa direban jirgin wuta.

Wakilin Aminiya da ke cikin jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna a safiyar Alhamis ya ce fasinjojin jirgin da ya baro Kaduna sun tsallake rijiya da baya, bayan jirgin da suke ciki ya taka nakiyar da su.

“Yau (Alhamis) da safe ina hanyata ta tafiya a cikin jirgin kasa, jirign da muke ciki ya taka nakiya, wanda ya yi sanadiyyar lalacewar layin dogon.

“Saura kadan jirgin kasan ya sauka daga kan titinsa, Allah ne kawai Ya kiyaye,” inji Sanata Shehu Sani, wanda shi ma fasinja ne a jirgin da ya taso daga Kaduna, yana siffanta abin da ya faru.

Matafiya a jirgin kasa sun yi cirko-cirko a safiyar Alhamis bayan tashin nakiyar a lokacin da jirginsu da ya taso daga Kaduna ya bi ta kan nakiyar.

Wakilin Aminiya ya ce daga baya jirgin ya samu karasawa zuwa Abuja bayan an sauya masa layi, amma jirgin da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna ba zai iya wucewa, sai dai jan shi aka yi ya koma.

Shehu Sani ya ce, “Jiya (Alhamis) ’yan bindiga sun kai wa jirgin kasa hari. Sun kuma dasa nakiya da ya lalata layin dogon da murfin injin jirgin.

“Sun bude wuta da nufin samun matukin jirgin da tankin man, amma a tsakanin yankin Dutse da Rijana, amma direban ya samu ya karasa tashar jirgin kasa da ke Rigasa a Kaduna.”