✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An daura auren jikar Ado Bayero da basaraken Yarabawa a Kano

An dai daura auren ne a gidan Madakin Kano da ke birnin Kano, kuma ya samu halartar manyan baki

Basaraken Yarabawa, Oluwo na masarautar Iwo, Oba Abdulrosheed Adewale Akanbi (Telu 1) a ranar Asabar ya auri, jikar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero, wato Gimbiya Firdaus Abdullahi.

 

An dai daura auren ne a gidan Madakin Kano da ke birnin Kano, kuma ya samu halartar manyan baki daga ciki da wajen jihar.

Sai dai wakilinmu ya lura cewa babu cincirindon mutane kamar yadda aka yi tsammanin samu a yayin bikin.

Taron dai ya samu halartar wakilin Mataimakin Shugaban Kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da Sanata Babafemi Ojudu, wanda shi ne mai taimaka wa Shugaban Kasa kan harkokin siyasa da Sarakunan Yarabawa na Kano da na Zazzau.

Angon dai ya biya Naira miliyan daya a matsayin sadaki, kuma an daura auren ne a gaban Madakin Kano mai ci, Yusuf Ibrahim Cigari.

Gimbiya Firdaus dai diyar marigayi Madakin Kano ce, Alhaji Abdullahi Sarki Sani Yola, kuma tsohon Bulaliyar Majalisar Dokokin Jihar Kano, Alhaji Mahmood Sani shi ne ya kasance waliyyin amarya, yayin da Babalaji na Iwo, Barista Ismail Oteyeku ya zama waliyyin ango.

Firdaus dai, wacce ’yar wan Sarkin Kano na yanzu, Alhaji Aminu Ado Bayero ce, tana da takardar karatun difloma a fannin girke-girke daga Kwalejin Fasaha ta Jihar Kano.

A baya dai ta taba yin aure, amma daga bisani mijin nata ya rasu.