✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daura auren masoya a sararin samaniya saboda COVID-19

Mutum kimanin 160 ne suka amsa goron gayyatar bikin auren da aka gudanar a sararin samaniya.

Wasu masoya a kasar Indiya sun dauki hayar jirgin sama don gudanar da bikin aurensu a wani yunkuri na kauce wa matakan kariya na cutar Coronavirus.

Mutum sama da 160 ne suka amsa goron gayyatar bikin auren da aka gudanar a sararin samaniya.

Wani dan kasar Indiya mai suna Donthu Ramesh (DonthuRamesh) ne, ya fara wallafa bidiyon a shafinsa na Twitter ranar Litinin.

Donthu, ya bayyana cewa masoyan sun dauki shatar jirgin na tsawon awanni biyu don bikin auren nasu.

Masoyan wanda suka fito daga yankin Tamil Nadu, wanda yana daga cikin yankunan da COVID-19 ta yi tsauri, mahukunta sun sanya dokar da haramta taron mutune da suka haura hamsin.

Tuni Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Saman Indiya, ta fara bincike don tabbatar da gaskiyar lamarin.