✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An daura auren Rukayya Dawayya da Afakallahu

A watannin baya ne Aminiya ta ruwaito cewa akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.

A yau Juma’a ne aka daura auren Shugaban Hukumar Tace Fina-finai na Jihar Kano, Isma’ila Na’Abba Afakallahu, da jarumar Kannywood Rukayya Umar Dawayya.

Idan ba a manta ba, a watannin baya ne Aminiya ta ruwaito cewa akwai soyayya mai karfi a tsakaninsu.

Tun kafin a soyayyar ta fito fili, jarumar ta rika sanya hotunan Afakallahu a shafinta na Instagram ba tare da nuna soyayyar ba, har zuwa lokacin da Aminiya ta fitar da labarin a  shirinta na Bidiyo mai taken Wata Sabuwa.

An daura daura auren ne da karfe 2:00 na rana a Masallacin Juma’a na Tishama, da ke Kano.

A kwanakin baya ne Aminiya ta kalato daga bakin angon cewa a auren nasu ba rakashewa kamar yadda al’adar auren ’yan Kannywood ta ke.