✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Daure Dan Tsohon Shugaban Kasar Mozambique

Kotu ta daure tsoffin shugabannin tsaro tare da dan tsohon shugaban kasar Mozambique shekaru 12 a gidan kaso

Bayan samun su da laifukan cin hanci, kotu ta yanke wa dan tsohon shugaban kasar Mozambique tare da tsoffin shugabannin tsaron kasar daurin shekaru 12 a gidan kaso.

Tsohon Shugaban Hukumar Leken Asirin kasar, Gregoria Leao, da na Sashen Leken Asirin Tattalin Arzikin Ma’aikatar Tsaron na baya Anotonio do Rosario, hadi da dan tsohon shugaban kasar, Ndambi Guebuza na daga cikin mutane 19 da aka tuhuma da cin hancin mafi girma a kasar.

Badakalar ta samo asali ne daga ciyo bashin wasu kamfanoni mallakin gwamnati da ke neman durkushewa har na Dala Biliyan Biyu ba bisa ka’ida ba a shekarun 2013 da 2014 daga bankunan kasa da kasa, don sayen jiragen ruwan kamun kifi da na sa sintiri.

Sai dai gwamnatin kasar ta boye wa majalisar dokoki da al’ummar kasar batun rancen, kamar yadda kafofin watsa labaran kasar suka bayyana.

Bayan bankado badakalar a shekarar 2016 ne Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) da sauran masu ba wa kasashe tallafi suka cire Mozambique daga jerin kasashen da suke tallafa wa.

Hakan ta sa kasar ta gaza biyan basussukan da ake bin ta tare da karyewar darajar kudinta a duniya.

Wani bincike mai zaman kansa da aka gudanar a kasar, ya gano cewa an karkatar da Dala miliyan 500 daga bashin, kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Da yake yanke hukunci kan shari’ar, Mai Shari’a Efigenio Baptista, ya ce tasirin laifukan zai ci gaba da bibiyar kasar har ’ya’ya da jikoki, tare da goga wa kasar kashin kaji a idon duniya.