Wata Babbar Kotun Tarayya mai zamanta a Kaduna, ta yanke wa wata mata Helen Carlos hukuncin zama kurkuku na wata 30 bayan da aka kama ta da miyagun kwayoyi.
Kotun karkashin jagorancin Mai Shari’a Mohammed Garba, ta yanke hukuncin ne bayan da matar ta amsa laifin da aka tuhume ta da shi.
- Dan shekara 5 ya mutu a motar makaranta a Saudiyya
- Ranar Yara Mata: A Najeriya aka koyar da mu kamar ’ya’yan turawa —A’isha Isma’il
Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ce ta gurfanar da matar a kotu don ta fuskanci hukunci daidai da laifin da ta aikata.
Kotu ta yanke wa matar hukuncin ne ba tare da wani zabi ba na biyan tara.
Kuma an yake mata zaman kaso na watanni 30 din ne duba da ba a taba kama ta da wani lafi a kotu ba sai a wannan karon.
Kotun ta gargadi matar kan ta guji jefa kanta cikin ta’ammali da miyagun kwayoyi idan ta kammala zaman kaso ta fito.
Tun farko, lauyan NDLEA, T.J. Atserhegh, ya shaida wa kotun cewa a ranar 14 ga Satumba ce jami’an hukumar suka damke Carlos a babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ya ce an kama ta ne dauke da kunshin tabar wiwi da kuma kwayar Taramol wanda hakan ya saba wa dokar kasa.
(NAN)