✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An daure matashi shekara 14 kan yi wa karamar yarinya fyade

Alkaliyar kotun ta gamsu da hujojjin da aka gabatar mata kan wanda aka yanke wa hukuncin.

Wata kotun majistare da ke zamanta Abeokuta a Jihar Ogun, ta yanke wa wani matashi dan shekara 20 hukuncin daurin shekara 14 saboda laifin yi wa ’yar shekara bakwai fyade.

Matashin ya musanta aikata laifin da ake tuhumarsa da shi, amma alkalin kotun, Misis I.O Abudu, ta ce masu gabatar da kara sun tabbatar da cewa ya aikata laifin.

Alkalin ta bayyana cewa ta gamsu da shaidun masu gabatar da kara, don haka ta yanke masa hukuncin daurin shekara 14 a gidan yari ba tare da zabin tara ba.

Tun da farko a lokacin shari’ar, wani jami’in hukumar sibil difens (NSCDC) mai gabatar da kara, ASC Adeola Oluwaseun, ya shaida wa kotun cewa wanda ake tuhumar, ya aikata laifin ne a watan Yuni.

A cewar mai gabatar da karar, wanda aka yanke wa hukuncin ya dauki yarinyar ne zuwa wani kango sannan ya yi lalata da ita.

Jami’an hukumar sibil difens ne suka cafke matashin bayan an shigar sa kara a kansa kan aikata laifin.

Tuni kotun ta ce laifin ya saba wa dokokin kare hakkin yara na Jihar Ogun na shekarar 2006.