✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ’yan acaba 29 shekara 3 a Zariya

Mai shari'a Madam Keziah Isaac Austin, wadda ta ce dukan wadanda aka samu da laifin sun amsa laifin ta ba su zabin biyan tarar N10,000…

Wata kotun gargajiya ta yanke wa ’yan acaba 29 hukuncin daurin shekara uku kowannesu, kan saba dokar haramta sana’arsu a Zariya, jihar Kaduna.

Mai shari’a Madam Keziah Isaac Austin, wadda ta ce dukan wadanda aka samu da laifin sun amsa laifin ta ba su zabin biyan tarar N10,000 ko zaman gidan yari.

Tun da farko dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa an kama ’yan acabar ne a wurare daban-daban a yankin Dan Magaji a Wusasa Zariya a ranakun 3 da 5 ga watan Disamba 2022.

Yunusa ya ce an kama su ne a yayin da suke gudanar da sana’arsu ta  haya da babura, wadda ta saba wa dokar Jihar Kaduna ta hana haya da kuma hawa babura.