✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ’yan damfarar intanet tare da kwace dukiyarsu

Wata Babbar Kotun Jihar Edo da ke birnin Benin ta yanke wa wasu barayin Intanet uku hukuncin dauri tare da kwace dukiyarsu.

Wata Babbar Kotun Jihar Edo da ke birnin Benin ta yanke wa wasu barayin Intanet uku hukuncin dauri tare da kwace dukiyarsu.

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ce ta gurfanar da su a gaban kotun bisa tuhumar aikata laifuffuka da samun dukiya ta hanyar karya a gaban Babbar Kotun Jihar inda Mai shari’a Efe Ikponmwonba ke alkalanci.

Bayan sauraren karar da gabatar da shaidu, Mai shari’a Ikponmwonba ya yanke wa Emeka hukuncin daurin shekara uku a gidan yari tare da zabin biyan tarar Naira dubu 200, yayin da Collins da Chukwudi aka yanke musu hukuncin shekara biyu a gidan yari ko kuma tarar Naira dubu 200 kowanensu.

Alkalin kotun ya bayar da umarnin a kwace wata mota kirar Marsandi GLK350 daga Emeka da kuma Naira miliyan 1 da dubu 932 da 893 da ke asusun bankinsa na Fidelity.

Har ila yau, za a kwace wayoyin wadanda aka yanke wa hukuncin da kudaden da suke cikin asusun ajiyarsu na banki a bankunan Sterling Bank da Keystone da First Bank da Wema saboda sun same su ne ta hanyar aikata laifuffuka.

Kuma kotun ta bayar da umarnin a rufe asusunan, inda Mai shari’a Ikponmwonba ya umarci wadanda aka yanke wa hukuncin su yi alkawari a rubuce na kasancewa masu kyawawan halaye daga yanzu.

Lauyoyin masu gabatar da kara, Ibrahim Mohammed da I.K. Agwai, sun yaba wa kotu kan yanke hukunci ga mutum ukun.