✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An daure ’yan majalisa 2 kan dukan takwararsu mai juna biyu a Senegal

An daure ’yan majalisa 2 kan dukan takwararsu mai juna biyu a Senegal

Wasu yan Majalisar Wakilan kasar Senegal biyu za su shafe wata shida a kurkuku bayan kotu ta same su da laifin dukan wata abokiyar aikinsu mai juna biyu a ciki lokacin da ake tafka muhawara a zauren majalisar kan kasafin kudin kasar.

’Yan majalisar wadanda maza ne, sun kai wa Amy Ndiaye duka ne bayan ta soki wani shugaban addini kuma jagoran wata jam’iyyar siyasa a kasar.

A hukuncin data yanke alkalin kotun ta kuma ce ’yan majalisar biyu Mista Mamadou Niang da Mista Massata Samb, su biya Uwargida Ndiaye Naira miliyan shida da dubu 600 (kwatankwacin Sefa miliyan biyar) a matsayin ramuwar cin mutuncinta da suka yi.

Dukan ’yar majalisar ya janyo kakkausar suka a fadin kasar, kuma ya haifar da mahawara kan ’yancin mata.

An yada bidiyon dukan a Intanet, inda ake iya ganin Mista Samb yana zuwa wurin da Uwargida Amy Ndiaye ke zaune kuma da isarsa sai ya kwada mata mari yayin da ake muhawara kan kasafin kudin a ranar 1 ga Disamban bara.

Ta mayar da martani ta hanyar jifansa da kujera, sai dai a daidai lokacin wani dan majalisar ya hambare ta a ciki. Rikici ya barke a zauren majalisar yayin da sauran mambobi suka yi kokarin kwantar da kurar.

Madam Ndiaye ’yar majalisa ce ta gamayyar jam’iyyun Benno Bokk Yakaar mai mulkin kasar, kuma ta suma jim kadan bayan dukanta a ciki, lamarin da ya sa aka yi fargabar cikin nata na iya zubewa.

Bayan an sallame ta daga asibiti, Madam Ndiaye ta ci gaba da zama a cikin kunci, kamar yadda lauyanta Boubacar Cisse ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Duk da bidiyon dukan da ’yan majalisar biyu suka yi wa matar, lauyoyinsu sun kafe cewa wadanda suke wakilta ba su aikata laifin da ake tuhumarsu ba.

Sun bukaci kotun ta tabbatar da cewa ’yan majalisar na da kariya ta doka daga fuskantar hukunci.

Daya daga cikin lauyoyinsu mai suna Abdy Nar Ndiaye ya shaida wa AFP cewa, “Za su ci gaba da zama a kurkuku zuwa lokacin da za a saurari daukaka karar da suka yi.”