✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dawo da dokar kullen COVID-19 a Najeriya

Dokar za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren Talata.

Gwamnatin Tarayya ta dawo da dokar hana zirga-zirga da nufin takaita yaduwar cutar COVID-19 a Najeriya.

Sanarwar ta kuma ba da umarnin rufe wuraren shakatawa, motsa jiki da da wuraren gudanar da babukuwa har sai abin da hali ya yi.

Dokar wadda ta haramta zirga-zirga daga kare 12 na dare zuwa karfe 4 na asuba, za ta fara aiki ne daga karfe 12 na daren Talata 11 ga Mayu, 2021.

Da yake sanar da hakan a yammacin Litinin, Manajan kula da Wadanda suka Kamu (NIM), na Kwamitin Shugaba Kasa (PSC) kan cutar COVID-19, Dokta Mukhtar Muhammad, ya ce ba a yarda mutum fiye da 50 su taru a wuri a lokaci guda ba.

Gwamnatin Tarayyar ta kuma umarci jami’an tsaro da tabbatar da bin dokar, wadda ta haramta shiga ofisoshin gwamnati ba tare da takunkumi ba.

Ta kuma bukaci jihohi su tabbatar da bin ka’idojin kariyar cutar COVID-19 da suka hada da bayar da tazara da sauransu, tare da gurfanar da masu karya dokar a gaban kotu domin su biya tara.

Ta kuma bukaci ma’aikatun gwamnati su takaita tafiye-tafiye sannan su koma da gudanar taruka ta bidiyo.

An dawo da dokar ne bayan samun hauhawar masu kamuwa da cutar ta COVID-19 da aka samu a kasasshen Brazil, Indiya, Turkiyya da sauransu.