✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dawo da hanyoyin sadarwar da aka katse saboda matsalar tsaro a Kaduna

Sai dai Gwamnatin Jihar ta ce har yanzu sauran matakan na nan daram.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta dage dokar  katse hanyoyin sadarwar da ta yi tun a watan Oktoba saboda hare-haren da ’yan bindiga suke kai wa wasu sassan Jihar.

Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan a ranar Juma’a.

A cewarsa, tuni Gwamnatin Jihar ta umarci kamfanonin sadarwa da su dawo da hanyoyin sadarwar da aka riga aka katse a baya.

A watan Oktoba ne dai gwamnatin ta dauki matakin katse layukan wayar a wasu sassan Jihar sakamakon yadda al’amarin rashin tsaro ya yi kamari a wasu yankunan Jihar.

Sai dai kuma duk da haka, matakin bai hana  ’yan bindigar  ci gaba da kai hare-hare ba, musamman a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Sai dai kuma Gwamnatin ta ce sauran matakan da ta dauka kamar na hana hawa babura da hana cin  kasuwannin mako-mako da kuma sayar da man fetur cikin  jarkoki har yanzu na nan daram.