✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dawo da kayan tallafin COVID-19 da aka yi warwaso a Filato

Wasu daga cikin mutanen da suka yi warwason kayan abinci na tallafin COVID-19 a Jihar Filato a yayin zanga-zangar #EndSARS, sun dawo da kayan da…

Wasu daga cikin mutanen da suka yi warwason kayan abinci na tallafin COVID-19 a Jihar Filato a yayin zanga-zangar #EndSARS, sun dawo da kayan da suka yi warwaso ga gwamnatin jihar tare da rokon gafarar a yafe masu laifin da suka yi.

Wadanda suka yi warwason kayan abincin, sun dawo da su ne zuwa ga gidan gwamnatin jihar, da ke birnin Jos a ranar Talata.

Da yake jawabi yayin da ya jagoranci wadanda suka dawo da kayan zuwa fadar gwamnatin Filato, Rabaran Ezekiel Dachomo, ya bayyana cewa ya jawo hankalin wadanda suka yi warwason kayan ne a wajen wani taron wa’azi da aka shirya a makarantar Sakandiren gwamnati ta Zang da ke garin Bukur, a Karamar Hukumar Jos ta Kudu.

Sakataren Gwamnatin Filato, Farfesa Danladi Atu lokacin da yake karbar kayan abinci na tallafin Covid-19 da aka dawo da su
Kayan abinci na tallafin Coronavirus da aka wawushe kuma aka dawo da su a Filato
Wadanda suka wawushe kayan abinci na tallafin Coronavirus da suka dawo da su a Jos

Ya ce a wajen taron wa’azin ya yi Allah wadai da wadanda suka yi wannan aika-aika, tare da nuna cewa wannan abu da suka aikata, zai iya jawo Allah ya yi fushi da su tare da al’ummar Filato, baki daya.

Rabaran Dachomo ya ce jin wannan wa’azi ne ya yi tasiri a zukatan sama da mutum dubu biyu da aka yi wannan warwarso, kuma ya kasance suna wajen wannan wa’azi.

Ya ce hakan ya sanya nan take suka ce zasu dawo da wadannan kayayyaki, tare da rokon gafarar Ubangiji da gwamnatin Filato kan wannan abu da suka aikata.

Ya yi kira ga gwamnan Filato, Simon Lalong ya yafewa wadannan mutane da suka dawo da wannan kaya.

Da yake karbar kayan a madadin gwamnan Filato, Sakataren gwamnatin jihar Farfesa Danladi Atu, ya yabawa Rabaran Dachomo kan kokarin da ya yi wajen ganin ya jawo hankalin wadannan mutane, kan abin da suka aikata har suka gane kurensu kuma suka nemi a yafe masu.

Ya ce wadanda suka yi wannan warwaso a yayin zanga-zangar ta EndSARS, ba kayan abinci kadai suka wawushe ba, sun hada har da manyan injina na biliyoyin naira.

Ya nuna farin cikinsa da wannan abu da wadannan mutane suka yi tare da alkawarin zai mika sakon su ga gwamnan jihar.