✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An dawo wa Najeriya N2.5bn daga kudin da Ibori ya sace

Najeriya ta karbo Fam miliyan 4.2 daga cikin kudaden daga kasashen waje.

Najeriya ta karbo Naira biliyan N2.4 daga cikin kudaden da iyalan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori suka wawure.

Attoni Janal kuma Ministan Shari’ah, Abubakar Malami, ya tabbatar da cewa Gwamantin Tarayya ta karbo Fam miliyan 4.2 kwatankwacin N2.438bn daga cikin kudin.

“Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna don dawo da kudaden Ibori a madadin Gwamnatin Tarayyar Najeriya,” inji mai Magana da ministan, Umar Jibrilu Gwandu.

Ya ambato ministan na cewa haakan, “Ya nuna irin kimar da Najeriya ta samu ta hanyar bayar da bayanan yadda aka ririta kudaden satar da aka kwato wajen aiwatar da ayyukan ci gaban jama’a.”

Gwandu ya kuma sanar a ranar Talata cewa an sanya kudin a cikin asusun Gwamnatin Tarayya na masumman, daidai da darajar canjin Naira a ranar 10 ga Mayu, 2021.