✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fanso mata 4 da jarirai da aka sace a Zariya

An fanso wasu mata hudu da jariransu biyu da ’yan bindiga suka sace a Cibiyar Kula da masu Tarin Fuka da Kuturta da ke Zariya.…

An fanso wasu mata hudu da jariransu biyu da ’yan bindiga suka sace a Cibiyar Kula da masu Tarin Fuka da Kuturta da ke Zariya.

Wata majiya mai tushe da ta bukaci a sakaya sunanta ta ce, an sako matan ne bayan kai kudin fansa da sabbin babura kirar CG guda biyu.

A ranar 3 ga watan Yuni ne ’yan bindiga suka kai hari Cibiyar Kula da Masu Tarin Fuka da Kuturta da ke Saye a gundumar Dutsen Abba ta Karamar Hukumar Zariya.

A yayin harin ne ’yan bindigar suka yi awon gaba da mutane goma cikin su har da wasu ma’aikatan asibitin biyar.

Wani ma’aikacin Cibiyar da ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa, wadanda aka tafi da su din sun hada da maza biyu da mata takwas da kuma jarirai na goye guda biyu cikin su har da dan wata hudu.

Sai dai a yanzu an sako matan hudu da goyansu bayan biyan kudin fansa tare da kai wa maharan babura biyu.

A yanzu haka mutane shida suka rage a hannun ’yan bindigar bayan fanso matan hudu da jarirai biyu kan kudin da ba a fayyace ba.

Ana iya tuna cewa, ’yan bindigar masu yawan gaske sun kai hari cibiyar ce da misalin karfe 12:30 na dare a ranar 3 ga watan Yuni, inda suka tare wata gada da ke kaiwa zuwa cibiyar.

A yayin haka ne kuma wasu daga cikinsu suka afka Cibiyar sai kuma wasunsu suka yi ruwan wuta a ofishin ’yan sanda da ke cibiyar a yankin na Saye.

Rukunin gidajen da aka shiga aka sace ma’aikatan
Cibiyar Kula da Masu Tarin Fuka da Kuturta da ke Zariya
Hanyar zuwa cibiyar da ‘yan bindigar suka tare a yayin kai harin.

Sai dai babu wanda ya mutu yayin harin da aka shafe sama da sa’a guda ana gudanar da shi a wannan rana.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mahukunta Cibiyar amma suka ki cewa uffan, inda suka nemi ya tuntubi iyalan wadanda aka sako.

Kazalika, har kawo yanzu hukumomin tsaro ba su ce komai a kan lamarin ba.