✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara ba ma’aikata mazan da matansu suka haihu hutu a Najeriya

Gwamnati ta ce hutun zai ba su damar shakuwa da jariransu

Gwamnatin Tarayya ta amince da fara ba ma’aikatanta maza wadanda matansu suka haihu hutun kwana 14.

Shugabar Ma’aikata ta Najeriya, Folasade Yemi-Esan, ce ta bayyana hakan ranar Litinin a cikin wata wasika da ta fitar dauke da kwanan watan 25 ga watan Nuwamba mai lamba HCSF/SPSO/ODD/NCE/RR/650309/3.

Wasikar mai taken, “Lissafa kwanakin hutu da kuma amincewa da hutun maza ma’aikatan gwamnatin da matansu suka haihu,” ta kunshi tanadin da kundin dokokin aikin gwamnati na shekara ta 2021, wanda ya amince da lissafa kwanakin hutu daga cikin kwanakin aiki.

“Gwamnati ta kuma amince da fara ba ma’aikatanta maza da matansu suka haihu, hutun mako biyu. Amma hutun kada ya wuce sau daya a cikin shekara biyu, kuma haihuwar kada ta wuce ta yara hudu.

“A inda kuma iyalan ma’aikaci namiji suka dauko rikon yaron da bai kai wata hudu ba, shi ma a nan mijin zai sami hutun kwana 14,” inji Shugabar Ma’aikatan.

Sai dai ta ce dole ne ma’aikacin ya hado da takardar likita da ke nuna ranar da ake tsammanin haihuwar ko kuma shaidar cewa ya dauko dan riko daga hukumar da ta dace ta gwamnati, kafin a amince da bukatar tasa.

Ta kuma ce dokar ta fara aiki na daga ranar 25 ga watan Nuwamban 2022.

Idan za a iya tunawa, a watan Satumban da ya gabata ne gwamnatin ta sanar da fara ba mazan hutun na kwana 14 don su sami lokacin kula da kuma sabawa da jariran nasu yadda ya kamata.

Ta ce hakan na da matukar muhimmanci saboda zai ba iyaye mazan damar shakuwa da ’ya’yan nasu tun suna jarirai, kamar yadda iyayensu mata ke yi.