✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara cin masu tuki suna daukar hoto tarar N100,000 a Birtaniya

Dokar ta tanadi tarar N50,000 ga masu jefar da filtar sigari a kan hanya

An fara aiwatar da sabuwar dokar cin tarar Naira dubu 100 ga masu daukar hoto ko bidiyo a yayin da suke tuki ta fara aiki a kasar Birtaniya.

Sabuwar dokar ta kuma tanadi tarar Naira 50,000 ga duk wanda aka kama ya jefar da filtar taba sigari a kan hanya daga cikin mota.

Dokar da ta fara aiki a ranar Lahadi tana daga cikin sabbin sauye-sauyen da Gwamnatin Birtaniya ta yi wa dokokin tuki a kasar, da nufin kare masu amfani da hanyoyi da kuma kare muhalli daga illar tabar da aka jefar.

Game da masu jefar da filtar sigari, dokar ta sanya tarar Fam 50 zuwa Fam (N25,000 zuwa N100,000) ga duk wanda aka kama da laifin.

Sai dai dokar ba ta haramta shan sigari a cikin mota ko wuraren taron jama’a ba a kan titi, ta taikaita ne a kan masu jefar da ragowar sigari barkatai a yayin da suke tuki.

Tun a shekarar 2003 gwamantin Birtaniya ta haramta yin waya ga mutane a yayin da suke tuki.

Wani jami’i a kamfanin hada-hadar kudi na CarMoney da ke Birtaniya, Andrew Marshall, ya ce sabbin, “Sabbin dokokin za su kai ga cin karin direbobi tarar karin kudi.

“Za kuma sa sanya masu amfani da hanyoyi su rika nuna sanin ya kamata; Kuma saba dokar babban laifi ne.”

Ya ci gaba da cewa, “Muna tunatar da masu amfani da hanyoyi su kasance masu lura wajen kiyaye dokokin hanya da kuma kare rayukan sauran masu matafiya.”