✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara daukar shirin Gidan Badamasi zango na 4

Muna fatan ya zo gareku da alkairi.

Rahotanni sun bayyana cewa an fara daukar sabon shirin Gidan Badamasi zango na hudu.

Mai Ba da Umarnin shirin, Falalu A. Dorayi ne ya sanar da hakan cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

A cewarsa, “Bisa horewar Ubangiji, Mun fara daukar shirin Barkwanci Gidan Badami 4 daga Dorayi Films & Distributing Ltd.

“Muna bukatar addu’ar masoya, Allah ya sa mu kare cikin nasara.
“Muna fatan ya zo gareku da alkairi,” a cewar sakon.
Shirin dai tashar Arewa24 ce ta saba hasa shi a duk ranar Alhamis.

Nazir Adam Salih ne ya tsara labarin, Falalu Doyari kuma ya shirya, Nasiru Ali Koki da Muhd M. I. Sardauna suka ba da umarni.

’Yan wasan sun hada da; Falalu Dorayi, Magaji Mijinyawa, Mustapha Naburaska, Umma Shehu, Hauwa Ayawa, Nura Dandolo, Ado Gwanja, Tijjani Asase, Hadiza Kabara, Aminu Mirror da sauransu.

Kamar yadda fostar sabon zangon ta nuna, jarumi Adam A. Zango zai fito a cikin sabon shirin.