✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara gyaran makabartar Gashuwa da ruwa ya yi wa barna

Binciken Aminiya ya gano akalla kabari 650 ne suka burma sakamakon ruwan sama.

Rahotanni garin Gashuwa da ke Jihar Yobe sun ce an fara gyaran makabartar garin wacce ruwan sama ya lalata.

Hakan na zuwa ne kasa da sa’o’i 24 bayan wani rahoto da Aminiya ta fitar kan yadda ambaliyar ruwan sama ya lalata kaburbura da dama a makabartar.

  1. Gobara ta kashe mutum 64 a wurin killace masu COVID-19
  2. An kashe mutum 222, an yi wa 20 fyade a wata 3 a Kaduna – Rahoto

Rahotanni sun ce akalla kaburbura 650 ne suka burma sakamakon mamakon ruwan sama da aka yi a karshen mako.

Ma’aikata yayin da suke sauke kayan aikin gyaran makabartar

Gwamna Jihar ta Yobe, Mai Mala Buni ne ya ba da umarnin gyaran makabartar bayan samun rahoton halin da ta ke ciki.

Buni ya bada umarnin fara gyaran ne karkshin Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA).

Ma’aikata yayin da suke sauke kayan aikin gyaran makabartar

Shugaban Hukumar a Jihar, Dokta Mohammed Goje ya shaida wa Aminiya cewar tuni aka kai kayan aikin da za a yi amfani gyara makabartar.

Kazalika, wani magidanci mazaunin yankin mai suna Yahaya Mato, ya shaida shaida wa wakilinmu cewar tuni mota ta jibge bulo da siminti don fara aikin.

“Mun tare hanyoyin da ruwa ya balle jiya, muna godiya ga gwamnatin Jihar Yobe kan daukar matakin gaggawa,” a cewarsa.