✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara jefa kuri’a a zaben Shugaban Kasar Angola

Masu rajistar zabe miliyan 14.7 ne za su yi alkalanci a zaben da ake kada kuri'a a rumfunan zabe 13,200 a fadin kasar.

Jama’ar Angola sun fara jefa kuri’ar zaben shugaban kasar a safiyar Laraba tsakanin Shugaba Joao Lourenco da madugun ’yan adawa, Adalberto Costa Junior.

Shugaba Lourenco na Jam’iyyar MPLA mai neman tazarce da kuma Adalberto na Jam’iyyar UNITA, kowannensu na neman goyon bayan miliyoyin matasa da talakawan kasar domin kai bantensa a zaben.

Masu rajistar zabe miliyan 14.7 ne za su yi alkalanci a zaben da ake kada kuri’a a rumfunan zabe 13,200 a fadin kasar.

Tun da sanyin safiya jama’ar kasar suka fita domin kada kuri’a a zaben da gamayyar ’yan adawa ke kokarin ganin sun amshe ragamar mulkin daga hannun gwamnati mai ci ta UNITA.

Ana zaton matasan kasar za su yi amfani da zaben wajen bayyana bacin ransu bisa yadda aka bar su cikin mawuyacin halin talauci, duk da arzikin mai da Allah Ya huwace wa kasar.

Jam’iyyar MPLA ta shafe kimanin shekara 50 tana mulkin Angola inda ake zaton zaben na 2022 zai yi tasiri wajen kara yaukaka ko sauya alakar kasar Angola da Rasha.

Wani bincike ya nuna har yanzu jam’iyyar tana da farin jini a wajen al’ummar kasar fiye da jam’iyyar adawa ta UNITA.

Sai dai tazarar da ke tsakaninsu babu yawa, don haka akwai yiwuwar UNITA ta yi nasara wanda hakan zai iya sauya akalar kawancen kasar daga Rasha zuwa kasashen Turai.

Tun bayan samun ’yancin Angola a 1975 take karkashin mulkin MPLA, wadda tun a shekarar 2017 Shugaba Joao Lourenco, yake jagoranta.

Amma alkaluman hasashen da Afrobarometer ya gudanar a watan Mayu ya nuna magoya bayan UNITA wadda Adalberto Costa Junior yake jagoranta sun karu zuwa kashi 22 daga kashi 13 da take da shi a 2019.

MPLA kuma na da kashi 29 cikin 100 a yayin da kusan kashi 50 na masu katin zabe a kasar ba su yanke shawarar dan takarar da za su zaba ba.