✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara kaura a wasu kauyukan Zariya saboda matsalar tsaro

Maharan sun harbe dam kasuwar har lahira sakamakon gardama da ya musu.

Wasu daga cikin al’ummomin garuruwan Zariya, musamman Dutsen Abba da kewaye sun fara yin kaura daga muhallansu saboda matsalar tsaro.

A daren ranar Laraba ne da misalin karfe 11:30 na dare, wasu ’yan bindiga suka sake komawa garin Saye Lemo da ke gundumar Dutsen Abba gidan wani dan kasuwa.

Gidan dan kasuwar na dab da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zariya, wanda a nan ne aka sace wasu mutane tare da kashe wasu a daren ranar Litinin.

’Yan bindigar sun kashe dan kasuwar sakamakon turjiyar da ya yi na kin binsu, wanda hakan ya sa suka harbe shi har lahira sannan suka yi awon gaba da ’ya’yansa guda uku; Fadila Habibu, Lawal Habibu da kuma Umar Habibu.

Farmakin da ’yan bindigar suka kai a daren ranar Litinin, ya yi sanadin ajalin dan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Rilwanu Aminu Gadagau.

Tuni aka yi masa sutura sannan aka birne shi a ranar Laraba.