✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara kidayar karuwai a Bauchi

Ana daukar bayanan matan a shirin taimaka musu da sana’o’in dogaro da kai.

Gwamnatin Jihar Bauchi ta ce ta fara kidayar karuwai na mako daya don taimaka musu su koyi sana’o’in dogaro da kai su bar harkar.

Kwamishinan Hukumar Hisbah ta Jihar Bauchi, Aminu Balarabe, ya bayyana hakan ne a yayin kaddamar da shirin tallafa wa mata masu zaman kansu a ranar Laraba a Bauchi.

Aminu Balarabe ya ce a karkashin shirin, gwamnatin jihar za ta taimaka wa masu son komawa wurin danginsu daga cikin matan.

Ya ce shirin ba shi da nufin cin zarafi ko nuna musu wariya, kuma gwamnatin jihar Bauchi ta fara shi ne bayan tattaunawa sosai da kuma la’akari da halin da karuwai ke ciki.

Hakan ne ya sa gwamnatin jihar shirya hanyoyi da kuma irin taimakon kudade da na tarbiya da matan suke bukata domin kyautata rayuwarsu.

“Gwamnatin Jihar Bauchi ta yanke shawarar samar musu da sana’o’in dogaro da kai da kuma jari domin ba su damar yin watsi da karuwanci.

“Wasu daga cikinsu wadanda ba ’yan asalin jihar ba za su iya komawa wurin iyayensu idan suna so; za mu tuntubi gwamnatocin jihohinsu mu mika musu su yadda ya kamata,” inji shi.

“Za a rarraba fom ga matan don su bayar da bayanansu na sirri kamar asalinsu da kuma dalilin da ya sa suka shiga harkar karuwanci.

“Ana kuma bukatar su nuna nau’in kasuwanci ko sana’ar da suke so,  Jihar kuma za ta dauki nauyin auren wadanda ke son yin aure ko kuma sake yin wani auren.

“Mun dukufa wajen aiwatar da Shari’ar Musulunci kamar yadda yake a cikin dokokinmu amma tare da kiyaye muhimman hakkokin dan Adam na kowane dan kasa,” inji kwamishininan.

Hafsat Aliyu, wacce ta wakilci mata masu zama kansu, ta bukaci gwamnatin jihar da ta cika alkawarinta tare da tabbatar da tallafa wa wadanda abin ya shafa yadda ya kamata.

Ta bayyana burinta na daina harkar kuma ta shiga ayyuka masu ma’ana don bayar da gudummawa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar.

A nasa jawabin, wani shugaban al’umma a yankin Bayangari da ke cikin garin Bauchi, Yakubu Bakawu, ya bukaci Hukumar Hisbah da kada ta tashe su daga yankin.

Shugaban Kungiyar masu Otal-otal din Najeriya (NHA) reshen jihar Bauchi, Mista Patrick Anyawu, ya ce akwai gidajen karuwai 41 a unguwar ta Bayangari.

Anyawu ya yaba wa shirin na tallafa wa karuwai, yana mai cewa karimcin zai kawar da talauci, rage aikata laifuka da kuma miyagun dabi’u a cikin al’ummar Jihar Bauchi.

Ya kuma yi alkawarin tallafa wa mazauna yankin domin saukaka gudanar da aikin.