✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara kwaso alhazan Najeriya zuwa gida

Jirgin farko na alhazan Najeriya sun baro Saudiyya zuwa gida a safiyar Juma'a

Jirgin farko na alhazan Najeriya da suka sauke farali a aikin Hajjin bana ya baro kasar Saudiyya zuwa Abuja.

A safiyar Juma’a jirgin farko na kamfanin Flynas ya dauko mahajjatan da suka fito daga Abuja daga filin jirgi na Jidda zuwa gida bayan sun kammala aikin Hajjin wannan shekara ta 2022.

Jirgin ya dauko mahajjata 423, kuma nan gaba kadan ake sa ran tasowar jirgi na biyu, har ila yau dauke da mahajjatan na Abuja.