✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara sauraron karar da Iyan Zazzau ya shigar

Don Iyan ya kalubalanci zaben Sarki tun da ba a bi al'adar Masarautar Zazzau ba.

Babbar kotun Jihar Kaduna da ke zamanta a Dogarawa Zariya, ta dage sauraren karar da Iyan Zazzau, Alhaji Bashir Aminu ya shigar yana kalubalantar nadin da aka yi wa sabon Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, zuwa ranar 27 ga watan Oktoban wannan shekara.

Kotun wanda mai shari’a Kabir Dabo ke jagoranta, ya ce a wannan rana ce kotu za ta ci gaba da sauraran bangarorin biyu bayan umarnin da kotu ta bayar na mika takardan kara ga wanda ake zargi wato bangarorin gwamantin Jihar Kaduna da Kwamishinan kananan hukumomi da Masarautu da masarautar Zazzau da masu zaben Sarki da kuma shi sabon Sarkin.

Masu karar sun garzaya kotu ne suna kalunbalantar gwamnatin jihar Kaduna bisa wannan nadi, inda suka nemi kotun ta yi watsi da shi kuma a bi tsarin da aka sani tun shekaru da dama da suka gabata na zaben Sarki a masarautar Zazzau.

Bayan an fito daga cikin kotun sai lauyan masu kara da Aminiya ta nemi jin ta bakin sa, Barista Samuel Atum inda ya ce suna wakiltar lauyan Iyan Zazzau ne mai suna Yunusu Ustaz kuma suna kalubalantar matakin da aka bi ne tunda ba a bi al’adar mutanen Zazzau kuma wanda aka nada bashi cikin wanda masu zaben Sarki suka zaba.

Yanzu dai za’a ci gaba da sauraron karar ne a ranar 27 ga watan Oktoba.