✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara sayar da babur mai tashi sama

Farashin babur din ya kai Naira miliyan 287.

Wani kamfanin kere-kere a kasar Japan ya fara sayar da babur mai tashi sama da ya kirkira a kan kimanin Dala 700,000, kimanin Naira miliyan 287.

Kamfanin A.L.I Technologies ya fara kera babur din da aka sa wa suna XTurismo Limited Edition ne tun a shekarar 2017, wanda a yanzu haka aka kammala har an fara sayarwa a kasar Japan.

Shugaban kamfanin, Daisuke Katano, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa za a iya keta hazo da babur din na kimanin minti 40, yana gudun kilomita 100 a cikin minti 40.

Yadda Babur din ke keta hazo a sararin samaniya

“Mun yi tunanin kera mashin din ne saboda biyan bukatar mutane masu son tuki a sama da kuma da saukaka zirga-zirga yayin kai agaji a lokacin da bukatar hakan ta taso a wuraren da motoci za su yi wahalar shiga,” a cewar shugaban kamfanin.

Ya kara da cewa suna so zuwa nan gaba masu amfani da motocin  kece  raini na zamani su koma amfani da mashin din.

Shugaban Kamfani Kere-keren A.L.I Technologies

Duk da cewa a yanzu an fara sayar da mashin din a kasar Japan an takaita zirga-zirga da shi zuwa wuraren tsere da kuma wuraren gwaji kafin daga baya gwamnati ta bayar da izinin amfani da shi a kan tituna.

A yanzu haka kofa a bude take ga duk mai bukatar sayen babur din daga ko’ina a duniya.