✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Rigakafin COVID-19 na jabu ya shiga kasuwanni —NAFDAC

NAFDAC ta ce babu kamfanin da aka ba wa izinin fara sayar da allurar rigakafin.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta ja hankalin ’yan Najeriya da su yi hattara da bata-garin da suka fara sayar da rigakafin COVID-19 na jabu.

Darakta-Janar na NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye, ta yi bayanin ne yayin da take ganawa da manema labarai a ranar Juma’a.

Ta ce “Mun samu rahoton wasu migayu sun fara sayar da allurar rigakafin coronavirus ta jabu. Don haka jama’a su yi hattara.

“Cutar sabuwa ce kuma dole ne rigakafin nata yana da wata illa. Kafin sahale wa wani kamfani wajen kasuwancin allurar dole ne sai mun gudanar da bincike.

“Duk da tabbacin da EUA ta bayar kan allurar rigakafin, dole NAFDAC ma ta yi nata binciken, don gano abubuwan da allurar ka iya haifarwa.

“Yanzu haka kwamitin kwararru da aka kafa, za su sanya ido kan sakamakon da zai fito bayan yi wa mutum allurar rigakafin,” cewar shugabar ta NAFDAC.

Ta kara da cewa babu wani kamfani ko ma’aikata da aka ba wa umarnin fara sayar da allurar rigakafin, domin dole sai an nemi sahalewar Hukumar kafin fara sayar da allurar.

Sannan ta ce har yanzu babu wani kamfani da ya nemi izinin fara sayar da allurar rigakafin, don haka duk allurar da aka gani da sunan rigakafin COVID-19 jabu ce ko kuma ba bisa ka’ida ake sayar da ita ba.

Har wa yau, ta ce hukumar ta zata fito da tsarin da za ta bi wajen bibiyar yadda rabon allurar zai kasance a fadin Najeriya.