✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara tantance masu ajiya a bankuna 42 da CBN ta rushe

Daga Litinin 21 zuwa Alhamis 24 ga Disamba za a tantance masu ajiyar da za a biya

Hukumar Kula da Bankuna da Kamfanonin Inshora ta Kasa (NDIC) ta fara tantance masu ajiya a bankunan 42 da aka rufe domin biyan su kudadensu.

Daraktar Tantance Hakkoki ta NDIC, Nurat Ajigbewu ta ce a ranar Litinin aka fara tantance masu ajiya a bankunan da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya kwace lasisi a ranar 12 ga watan Nuwamba.

“NDIC mai alhakin rufe bankunan da aka kwace wa lasisi a hukumance ta fara tantance masu ajiya a bankunan da ke da inshora domin biyan su kudadensu.

“Domin kammala wannan aiki hukumar na kira ga daukacin masu ajiya a bukanan da aka rufe dsu ziyarci rassansu domin ganawa da jami’an NDIC da ke kasa domin a tantance hakkokinsu dagar ranar Litinin 21 zuwa Alhamis 24 ga Disamba, 2020,”

Sanarwar da Kakakin NDIC, Bashir A. Nuhu ya fitar ta bukaci masu ajiyar da abin ya shafa da su je da takardun shaidar ajiya a banki, da wata takardar shaida domin saukake tantacewar.

Sunayen kananan bankunan da CBN ta rufe din a fadin Najeriya su ne:

 1. Hedgeworth Micro Finance Bank
 2. Future Growth Micro Finance Bank
 3. Bagwai Micro Finance Bank
 4. Ere City Micro Finance Bank
 5. Cafon Micro Finance Bank
 6. Akcofed Micro Finance Bank
 7. Gufax Micro Finance Bank
 8. Partnership Micro Finance Bank
 9. ICB Micro Finance Bank
 10. Onima Micro Finance Bank
 11. Hometrust (Nations) Micro Finance Bank
 12. Ringim Micro Finance Bank
 13. Bigthana Micro Finance Bank
 14. Rogo Micro Finance Bank
 15. Makoda Micro Finance Bank
 16. Takai Micro Finance Bank
 17. Bebeji Micro Finance Bank
 18. Ajingi Micro Finance Bank
 19. Garko Micro Finance Bank
 20. Kangiwa Micro Finance Bank
 21. Augie Micro Finance Bank
 22. Mopa Micro Finance Bank
 23. Solid Base Micro Finance Bank
 24. Ultimate Benefit Micro Finance Bank
 25. Ovidi Micro Finance Bank
 26. Kirfi Micro Finance Bank
 27. Credit Express Micro Finance Bank
 28. King Solomon Micro Finance Bank
 29. Riggs Micro Finance Bank
 30. Billionaire Blue Bricks Micro Finance Bank
 31. Susu Micro Finance Bank
 32. Wealthstream Micro Finance Bank
 33. Aguda Titun Micro Finance Bank
 34. Sapphire Micro Finance Bank
 35. Metro Micro Finance Bank
 36. Mountain Top Micro Finance Bank
 37. Unyogba Micro Finance Bank
 38. Wapo Micro Finance Bank
 39. Ibogun Micro Finance Bank
 40. Korede Micro Finance Bank
 41. Ahetou Micro Finance Bank
 42. Fufore Micro Finance Bank