✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An fara yi wa fursunoni rigakafin cutar coronavirus

Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya (RBC) da kuma Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali a kasar Rwanda, sun fara yi wa dattawan fursunoni allurar rigakafin cutar…

Cibiyar Nazarin Kiwon Lafiya (RBC) da kuma Hukumar Kula da Gidajen Gyara Hali a kasar Rwanda, sun fara yi wa dattawan fursunoni allurar rigakafin cutar Coronavirus da kuma masu fama da wasu cututtukan na daban.

Babban Kwamishinan Hukumar Gidajen Gyara Hali na kasar, George Rwigamba ne ya bayyana hakan a gidan yarin Nyarugenge da ke Kigali, babbar birnin kasar.

Ya ce an fara ne da Kurkukun Nyarugenge inda za a yi wa fursunoni 2,077 rigakafin cutar Coronavirus kuma ana sa fadada rigakafin zuwa ga sauran fursunonin da suka kai shekara sittin ko suka haura.

Rwigamba ya ce daga cikin fursunonin da za a yi wa rigakafin akwai kuma masu fama da wasu cututtukan na daban da ke zaman cin sarka a sauran gidajen yarin da ke fadin kasar.

Fursunoni 12,000 ake tsammanin za a yi wa rigakafin cikin ’yan kwanaki masu zuwa a cewar Rwigamba a yayin da tabbatar da kiyaye dokar bayar da tazara ya zamanto daya daga cikin manyan kalubalen da ake fuskanta a gidajen yarin.

RBC a ranar Talata ta sanar cewa tuni aka fara yi wa masu motocin haya da masu gadi allurar rigakafin a birnin Kagali.

A ranar Juma’ar da ta gabata ce aka fara yi wa gama gari allurar rigakafin cutar Coronoavirus ta Oxford-AstraZeneca da Pfizer a kasar Rwanda bayan an fifita wasu rukunin mutane da aka fara yi wa rigakafin a ranar Laraba.

Daga cikin rukunin farko na mutanen da aka yi wa rigakafin a kasar akwai ma’aikata masu fifikon muhimmanci ciki har da na lafiya da kuma mutanen da suka haura shekara 65 da masu fama da wasu cututtukan na daban.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya ruwaito cewa, fiye da mutane 200,000 aka yi wa rigakafin a kididdigar da RBC ta fitar a ranar Litinin.