✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An fara yi wa ’yan Nijar mazauna Najeriya rajistar zabe

Jami'an za su shafe mako biyu a jihar domin su yi aikin rajistar.

An fara yi wa al’ummar Jamhuriyar Nijar mazauna Najeriya rajistar katin zabe a Kalaba, babban birnin  Jihar Kuros Riba a ranar Litinin.

Ayawain na mutum biyu masu yin rajistar, karkashin jagorancin Adamou Amadou za su shafe mako biyu a jihar domin su yi aikin rajistar.

Adamou Amadou, jagoran tawagar ya shaida wa Aminiya cewa, “An turo mu ne daga Ofishin Jakdancin Jamhuriyar Nijar da ke Abuja zuwa Kuros Riba domin muyiwa ’yan asalin Jamhuriyar Nijar rajistar katin zabe.”

Ya ci gaba da cewa, “Za mu shafe mako biyu a nan muna yin rajistar kuma duk inda dan Nijar yake ya samu labarin za mu zo domin Aikin.”

Jami’in ba bayyana cewa idan suka kammala da Jihar Kuros Riba za su tafi garin na Uyo na Jihar Akwa Ibom domin suci gaba da yin aikin a can.

Shuhaban Kungiyar Kasar ’Yan Nijar mazauna Kuros Riba, Nasiru Ishaqa, ya bayyana matakin da gwamnatun kasarsu ta dauka na turo wakilai a yi musu rajista da cewa “Abin farin ciki ne, abin a yaba  ne.

“Zan zan tabbata sauran ’yan Nijar mazauna manyan garurukan Ikom da Ogoja su ma an yi musu rajistar,” in ji shi.

Al’umar sun fara kwarara zuwa wurin da ake yin rajistar a Unguwar Hausawa da ke layin Bagobiri a garin Kalaba.